Kwango: Mutum 8 sun mutu a zanga-zanga | Labarai | DW | 31.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwango: Mutum 8 sun mutu a zanga-zanga

A Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango an tabbatar da mutuwar mutane takwas a yayin da ake zanga-zangar adawa da tsawaita mulkin Shugaba Joseph Kabila da kungiyar kiristoci 'yan Katolika ta shirya a biranen kasar.

Jama'a da dama sun yi kunnen uwar shegu da umarnin gwamnati na hana gudanar da zanga zangar. Kungiyar Kiristoci mabiya darikar Katolika ta kasar ce ta kira al'umma zuwa ga shirya zanga-zangar a duk fadin kasar a wannan Lahadi bayan kammala taron addu'oi na mako a cikin mujami'u. Duk da kokarin jami'an tsaro da suka kutsa cikin mujami'un tun a lokacin da jama'a ke gudanar da addu'o'i ta hanyar anfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa su bai hana su gangamin da ya kai ga samun asarar rayukan mutane takwas tare da jefa kasar cikin sabon rudani.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito mutuwar mutum daya a yankin Kasai inda sojoji suka bude wuta kan rukunin wasu Kiristoci mabiya darikar Katolika da ke shirin gudanar da zanga-zanga, yayin da a birnin Kinshasa 'yan sanda suka kama wasu hadiman coci guda 12 a bakin wata mujami'ar tsakiyar birnin lokacin da suke yunkurin soma zanga-zangar ta yau.

Tun a yammacin wannan Asabar mahukuntan kasar suka bai wa kamfanonin salula umurnin katse layikan sadarwar intanet sabili da abin da suka kira dalilai na tsaron lafiyar kasa kuma yanzu haka kafofin aikawa da sakonnin SMS da ma na whatsApp sun daina aiki a fadin kasar.