1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan jaridu na fuskantar kalubale a Kwango

Salissou Boukari
November 2, 2016

Wata kungiya da ke kula da kare hakin 'yan jaridu a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango JED, ta fitar da rahoto a wannan Laraba, inda ta soki cin zarafi da ake yi wa wasu 'yan jarida a kasar.

https://p.dw.com/p/2S3tF
Journaliste en danger Reporter ohne Grenzen Büro im Kongo Zwischen Anspruch und Wirklichkeit: Mangelhafte Pressefreiheit in der Demokratischen Republik Kongo
Hoto: DW

Kungiyar mai zaman kanta ta (JED ), ta ce wannan lokaci shi ne mafi muni ga ayyukan 'yan jaridu a kasar ta Kwango, kuma ta ce ta samu tattara nau'i-nau'i na cin zarafin 'yan jaridu har sau 87 a kasar a wannan shekara ta 2016.

A hannu daya kuma tawagar jakadun kasashe 15 membobi a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya za ta kai wata ziyara a birnin Kinshasa daga ranar 10 zuwa 14 ga wannan wata na Nuwamba. Wannan tawaga dai za ta kasance a karkashin jagorancin jakadun kasashen Faransa, Senegal da kuma Angola, inda za su ziyarci biranen Goma, da Beni domin saduwa da shugaba Kabila, da kuma shugabannin 'yan adawan kasar.

Sannan tawagar ta kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na iya tilasta cewa 'yan kasar ta Kwango zu zabi ranar da ta dace a yi zabe, ba tare da shugaban kasar Kabila ya tsaya takara ba.