1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zarge-zarge kan shirin zabe a Kwango

Ramatu Garba Baba LMJ
December 28, 2018

A ranar Lahadi 30 ga watan Disamba 2018 ake gudanar da babban zaben kasa a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

https://p.dw.com/p/3Ak7Y
DRC Präsident Joseph Kabila
Shugaban Joseph Kabila na Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Reuters/K. Katombe

A makon da ya gabata ne dai mahukuntan na Kampala suka sanar da dage zaben da mako guda. Zaben da a baya aka shirya gudanar da shi a ranar 23 ga wannan wata na Disamba, an dage shi zuwa 30 ga watan na Disamba. Baya ga haka, an kuma dage zaben wasu yankuna a sanadiyyar yakin da ake da cutar Ebola da kuma batun masu tayar da kayar baya a kasar. Wannan matakin ma dai ya kuma haifar da rudani. A wata hira ta musamman da wakilin DW, Shugaba Joseph Kabila ya yi karin haske kan dalilin daukar matakin, duk kuwa da cewa jam'iyyun adawa da ma al'ummar yankunan, sun zargi hukumar zaben kasar CENI da daukar matakin bisa wasu dalilai na siyasa. Sai dai Shugaba Joseph Kabila ya ce lafiyar al'umma ke sahun gaba:

Kongo Ebola Behandlungszentrum in Bikoro
Cutar Ebola na daga cikin dalilan dage zabeHoto: picture-alliance/AP Photos/UNICEF/Mark Naftalin

''Ai hukumar zabe ta riga ta fayyace gaskiyar lamarin, CENI ta fahimtar da kowa cewa an dage zaben har zuwa lokacin da za a iya shawo kan annobar Ebola, kuma ba ya ga haka ta ce za a iya gudanar da zaben a watan Maris na shekara mai kamawa lokacin da ake ganin an riga an kammala dakile cutar.''

Ba ya ga batun Ebola Shugaba Kabila ya ce abu ne mai wuya a gudanar da zabe a wuraren da ake fuskantar barazanar tsaro kamar yadda lamarin ya ke a yanzu.

Kokarin kare rayuka

Ya ce: Batu na biyu shi ne tsaron rayukan jama'a, kun sani kuma kowa ya sani muna fama da rikici inda ake kashe mutane musamman a Beni, kuma ba fararen hula kadai ba mun rasa sojojinmu da ke yakar 'yan tawaye na kungiyar ADF da ma na wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya. Wadannan muhimman batutuwan biyu ne hukumar ta CENI ta yi la'akari da su kafin daukar matakin.''

Demokratischen Republik Kongo | Wahlkommision |  Wahlautomat
Zargin hukumar zaben Kwango CENI da shirin sake dage zabeHoto: DW/F. Quenum

Sai dai duk da wadannan hujjojin da Shugaba Kabila ya bayar, mazauna wadannan biranen sun ki amincewa da hakan ganin a wannan yanayin ne 'yan siyasa suka gudanar da yakin neman zaben, ba ya ga haka mutane na iya zuwa duk inda suka ga dama kama daga taro na addini zuwa cin kasuwa. Ba ka ganin in har za a iya gudanar da yakin neman zabe to babu dalilin ace ba za a iya gudanar da zaben kansa ba. To ko mai zai ce kan wannan zargi?

"Aah.... kamar yadda kowa ya sani ne, zaben na bana za a yi amfani da sabuwar na'ura , wanda hakan na nufin kowa zai zabi dan takarar da ya ke so ta hanyar amfani da na'ura guda. Matsalar ita ce, idan aka sami mutum guda da cutar Ebola ya kuma yi amfani da na'urar da mutum kusan dari biyar ko shida za su yi anfani da ita, kaga ai daruruwa sun kamu da cutar kenan. Ba kamar coci ko kasuwannin ba ne don babu irin wannan mu'amala, saboda haka gwamnati ba za ta amince a yada cutar Ebola a tsakanin al'umma ba."

Daga karshe dai shugaba Joseph Kabila ya kawar da zargin cewa, akwai wata sabuwar makarkashiya kan shirin sake dage zaben na ranar Lahadi, a cewarsa babu dalilin da zai ma hana a gudanar da zaben da ke tafe a karshen watan na Disamba.