1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sake dage zaben shugaban kasa a Kwango

Abdul-raheem Hassan RGB
December 21, 2018

Zanga-zanga ta barke a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo a sakamakon matakin da hukumar zaben kasar CENI ta dauka na sake dage ranar gudanar da zaben shugaban kasar daga 23 ga watan Disamba zuwa 30 ga watan na Disamba.

https://p.dw.com/p/3AUZG
Proteste im Kongo
Hoto: Reuters/K. Katombe

Matasa da sauran al'umma sun fantsama kan titunan Kinshasa babban birnin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango suna zanga-zangar nuna adawa da matakin dage lokacin zaben shugaban kasa da hukumar zaben kasar ta yi zuwa 30 ga wannan wata na Disamba da muke ciki. Mafi akasarin matasan da ke zanga-zangar sun nuna kosawa ne kan rashin aiki da kyakyawan yanayi na samun makomar rayuwa mai kyau cikin shekaru 18 na mulkin Shugaba Joseph Kabila.

Proteste im Kongo
Hoto: Reuters/K. Katombe

Hukumar zaben dai ta kafa hujjar sake dage ranar zaben ne kan rashin isowar wasu daga cikin kayan aiki zuwa rumfunan zabe a sassan kasar. Hukumar ta kuma ce gobara ta kama wurin ajiyar kayan zabe a makon jiya da ya barnata sama da takardun kada kuri'un birnin Kinshasha miliyan guda.

Gabanin zaben Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga bangaren gwamnati da na 'yan adawa da su guji haddasa tashe-tashen hankula a lokutan zabe ko bayan zaben. Tun daga shekarar 2016 al'ummar Kongo ke fatan sake zaben sabon shugaba, amma kafewar Shugaba Kabila kan mulki na tsawon shekaru 18 bayan gadar mahaifinsa, na zama karfen kafa ga harkokin zaben kasar.