1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin fitar da dan takara daga masu mulki

Salissou Boukari MNA
June 8, 2018

Wani taron majalisar ministoci a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango ya bai wa shugaba Joseph Kabila nauyin jagorancin wata hadaka ta jam'iyyun da ke mulki a kasar da aka kira FCC "Front Commun pour le Congo."

https://p.dw.com/p/2zAMr
Kongo Präsident Joseph Kabila
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Bompengo

Ga tsarin da aka yi dai wannan hadaka za ta fitar da dan takara daya tilo a zaben shugaban kasar mai zuwa. Sai dai kuma babbar fargabar da ake yi, ita ce ta ko shugaba Kabila da wa'adin mulkinsa ya kawo karshe tun daga ranar 20 ga watan Disamba na 2016 zai sake tsayawa takara.

A ranar 23 ga watan Disamba aka shirya gudanar da zabukan kasar ta Kwango, kuma daga ranar 25 ga watan Yuli mai zuwa ake soma ajiye takardun 'yan takarar da za su nemi shugabancin kasar. Sannan a ranar 19 ga watan Satumba a wallafa jerin sunayen 'yan takarar.

Sai dai shugaba Joseph Kabila ya ce zai yi biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar, amma kuma bai sanar cewa ko ba zai sake tsayawa takara ba.