An yi sulhu a tsakanin Ruwanda da Kwango
July 6, 2022Talla
Shugabannin kasashen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Ruwanda sun amince sun kawo karshen zaman doya da manjar da suka kwashe makonni suna yi. Fadar mulkin Kwango da ke birnin Kinshasa a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce an cimma wannan matsaya ce a wannan Laraba.
Sanarwar sasancin Kwango-Kinshasa da Ruwandan dai ta ce kasashen sun tsara yadda za a kawo karshen ayyukan 'yan tawayen M23 da ke halaka musu jami'an tsaro da fararen hula.