1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango: Dan shugaban kasa ya wawashe kudaden gwamnati

Abdourahamane Hassane RGB
August 8, 2019

Kungiyar Global Witness ce ta fidda rahoto inda a ciki ta zargi Christel Denis Sassou Nguesso da laifin yin sama da fadi da makudan kudaden gwamnati

https://p.dw.com/p/3NWXr
Denis Christel Sassou-Nguesso
Hoto: Wikipedia/VOA/A. Séverin

Wata kungiyar mai zaman kanta ta Birtaniya Global Witness mai fafufutukar yaki da cin hanci ce, ta fitar da rahoton, wanda a ciki ta zargi dan Shugaban Kwango Denis Christel Sassou-Nguesso da laifin yin sama da fadi da makudan kudaden daga asusun betalmanin kasar ta hanyar.

Batun yaki da cin hanci wannan shi ne abu na farko da Shugaban Kwango Denis Sassou Nguessou ya sha alwashin zai kawar, a cikin jawabin da ya yi a shekarar bara ya ambato cewar, ya san al'ummar Kwango sun kagu su gani an tsamo tare da hukunta masu laifin aikata cin hancin ba tare da an nuna bambamci ba.

Sai dai kwatsam, wani rahoton da ta bayyana wata kungiyar da ta shahara wajen yaki da cin hancin ta Kasar Birtaniya Global Witness, ta zargi dan shugaban Kwango Christel Sassou Nguesso, da laifin yin sama da fadi na kudade miliya 50 na Dala daga asusun betalmanin kasar kwatankwancin Euro miliyan arba'in da hudu da dari biyar, ta hanyar kakafa kamfanonin bogi a cikin kasashe dabam-dabam tsakanin shekara ta 2013 zuwa 2014.


Christel Denis Sassou wanda ake yi wa lakabi da sunan ''Kiki mai man fetir'' shi ne shugaban kamfanin samar da man fetir na Kwangon tun a shekara ta 2011 kana mamba a cikin jamIyyar da ke yin mulki. A shekara ta 2007 Kungiyar Transparency reshen Faransa ta bayyana shugabannin kasashen Afirka biyar wanda suka saci kudade suka saye manyan gidaje na alfarma a Faransa. Daga cikin shugabannin kuwa har da shugaban na Kwango Denis Sassou Nguesso. 


Kasar ta Kwangon, ita ce  kasa ta uku mafi arzikin man fetir a nahiyar Afirka.Wannan tabargazar da aka bankado ta kara zubar da martanin Shugaban Kwangon, wanda ya sha alwashin yaki da cin hanci, abin da ya sa ake ganin da wuya mai bunu a gindi ya je kishin wuta.