Kwanaki 100 na mulkin Trump | Siyasa | DW | 28.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kwanaki 100 na mulkin Trump

A wannan Asabar ce shugaba Donald Trump ke cika kwanaki 100 cif a karagar mulkin Amirka. Shin ko yaya manufofin shugaban suka shafi gudanarwar mulki da kuma mu'alamala da kasashen waje?

Mafi sassaucin kwatance na kwanaki 100 na shugaba Trump a karagar mulki shi ne bayanin Eric Gomez na cibiyar kwararru kan nazarin manufofin kasa da kasa Cato. Ya ce kwanaki 100 na farko na shugaba Donald Trump a fadar White House musamman ta fuskar manufofin ketare ba za ka iya rarrabe shi da na magabacinsa Barack Obama ba. Dalili kuwa a cewarsa shi ne Trump na gwama siyasa da harkoki na diplomasiyya dana kuma na soji. Ya ce babbar matsala ita ce, ba za ka iya yin hasashe kai tsaye kan manufofinsa ba saboda shugaba Trump yana yawan sauya ra'ayinsa, abin da kuma ya sa yake yin hakan shi ne bai fahimci makamar manufofin kasashen waje ba ne.

"Ya ce Ina jin matsalolin da muke gani a yanzu a dangane da yadda yake sauya matsayi. Galibin wadannan kwan gaba kwan baya da yin amai ya lashe da suke fitowa daga gare shi, Ina gani Trump bai fahimci abinda yake fada ta fuskar manufofin kasashen waje ba."

Shi ma dai Michael Werz na kwararru masu sassaucin ra'ayi a cibiyar nazarin cigaban Amirka wato CAP a takaice, yana da makamancin ra'ayi irin na Gomez. Ya ce a misali game da dangantaka da China, ko da aka yi masa tambaya mai sarkakiya kan ko Taiwan mallakin China ne, ba tare da yin cikakken nazari da tunani mai zurfi ba, nan take a wannan hira da 'yan jarida ya sauya matsayin da Amirka ta shafe shekaru 40 a kansa ya dangana yankin ga China lamarin da ke nuni da cewa ba shi da mashawarta na kwarai a cewar Michael Werz. 

"Ya ce shugaban yana kewaye da mashawarta ne masu ra'ayin mazan jiya ko ma a ce masu riko da akida ta ra'ayin rikau, domin idan ka duba ko da a ma'aikatar harkokin waje da tsaro da kuma ta muhalli, wadanda ke rike da shugabancin ma'aikatun mutane ne wadanda basa sauraron shawara."

To ko yaya manazartan ke kallon manufofin ketare na Amirka karkashin Donald Trump?

Eric Gomez na cibiyar kwararru kan nazarin manufofin kasa da kasa Cato ya ce manufofin na barazana ta fannin soji. A cewarsa luguden bama bamai da Amirka ta yi wa filin jirgin saman Siriya da matsayinta kan kungiyar IS a Afghanistan da kuma batun cewa Amirka za ta baiwa Yemen makamai a yakin basasar da ta ke yi, dukkan wadannan takala ce da suka kamata Amirka ta jikinta.

Jack James na sashen nazari mai zurfi kan Jamus a Jami'ar John Hopkins da ke Amirka, ya ce idan ba a yi hattara ba rikicin da ke neman kunno kai game da Koriya ta arewa na yin muni matuka. Ya ce Koriya ta arewa ba ma kawai ta mallaki makamin nukiliya bane kadai, a'a tana mai kera makamai masu linzami da ke cin dogon zango, inda ya kwatanta halin da ake ciki na Koriya ta arewa da rikicin kasar Cuba da ya faru a shekarar 1962 lokacin da shugaban Amirka John F Kennedy ya nemi dakile makaman tarayyar Soviet a Cuba. To sai dai a cewar James kamun ludayin Trump game da manufofin ketare ya nuna rashin kwarewa.

"Ya ce akwai alamar bai shiryawa aikin ba, ka dai san irin mutanen da yake kewaye da su, ba mutane bane da za su nusar da shi alkiblar da ta dace ko bashi shawarar daukar hukuncin da ya dace ba.

 

Sauti da bidiyo akan labarin