Kwan gaba kwan baya a yaki da Boko Haram | Siyasa | DW | 08.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kwan gaba kwan baya a yaki da Boko Haram

Hare-haren da kungiyar Boko Haram suka kai jihar Yobe sun nuna cewa sun dauki sabon salo, amma ba'a kai ga tantance ko nasara aka yi kansu ba, ko kuwa sun kara karfi ne

Akalla mutane 17 suka hallaka a hare-haren kunar bakin waken da aka yi a yankin area maso gabashin Najeriya, a daidai lokacin da kungiyar Boko Haram ta fitar da wani fei-fein bidiyo, inda take cewa shugabanta na da rai kuma yana nan ya jagoranta da kuma bin kadin lamura. A bayanin da ya yi wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, shugaban Hukumar Agajin Gaggawa ta NEMA ya ce daga cikin hare-haren wanda aka kai Damaturu ne ya fi muni inda mutane 14 suka hallaka wasu 10 kuma suka yi munanan raunuka.

A shekaru shidan da Boko Haram ta kwashe tana kai hare-hare, ta kai da yawa jihar Yobe. A watan da ya gabata ma, wata yarinyar da aka zaci shekarunta 12, ta kashe mutane shida tana daure da jigidan bam a wajen wata tashar mota.

A yanzu haka dai gwamnan jiharYoben Ibrahim Gaidam ya ce za su kara inganta matakan tsaro, kuma ya kira hare-haren aiyukan rashin imani. Duk da cewa ba'a riga an dauki alhakin wannan hari ba, ya zo ne bayan da kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin hare-haren da aka kai Abuja, babban birnin tarayyar Najeriyar.

Dakarun Najeriyar dai sun yi ikirarin nasarori a yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram kuma sun ce an kashe masu tayar da kayan bayan da dama lokacin wata arangama da aka yi. Mai magana da yawun rundunar sojin kasar Sani Usman ya ce mayakan sun yi yunkurin kai hari kan rundunar sojin da ke Goniri kilometa 60 daga kudu maso gabashin Damaturu amma ba su yi nasara ba.

Sauti da bidiyo akan labarin