1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwamitin sulhu na MDD zai tura dakaru Bangui

April 10, 2014

Membobin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya guda15, sun amince da tura dakaru zuwa Afirka ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/1Bg2F
Hoto: MIGUEL MEDINA/AFP/Getty Images

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya kada kuri'ar amincewa da tura dakaru a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, a kalkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya na Minusca, a wani mataki na kokarin kawo kashen rikicin dake ruruwa a wannan kasa.

Yarjejeniyar mai lamba 2149 ce ta tsara cewa za'a aika dakaru a kalla dubu 10 daga cikin su sojoji 240 masu sa'ido, da manya-manyan hafsoshin soja 200, da jamiyan tsaro na yan sanda 1800, sannan da wasu kwararru soja guda 20 masu kula da gidajan fursuna.

Ga baki dayan membobin kwamitin sulhun 15 ne dai, suka amince da wannan tsari, sannan kwamitin sulhun ya baiwa dakarun kasar Faransa 2000 dake wannan kasa, izinin dafawa dakarun na Majalisar Dinkin Duniya na Minusca, da zasu canji dakarun kungiyar Tarayyar Afirka na Misca dubu biyar da 600, a ranar 15 ga watan Satumba mai zuwa.

Kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniya, yayi fatan ganin an samu kasancewar dakarun Misca masu yawa cikin sabin dakarun na MDD na Minusca.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu