Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya zaɓi magajin Kofi Anan. | Labarai | DW | 09.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya zaɓi magajin Kofi Anan.

Rahotannin da muka samu daga birnin New York ba da daɗewa ba sun ce kwamtin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya zaɓi ministan harkokin wajen Korea Ta Kudu, Ban Ki-Moon, tamkar magajin babban sakataren Majalisar mai barin gado, Kofi Anan. Bayan ka da ƙuri’un zaɓan Ki-Moon da mambobin kwamitin suka yi, jakadan ƙasar Japan a Majalisar Ɗinkin Duniyar, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin sulhun mai ci yanzu, Kenzo Oshima, ya ce mambobin sun yi kyakyawan zaɓi. Amma dai har ila yau dai, bisa kundin tsarin aiki na majalisar, sai babban taro na ƙasashe ɗari da 92 mambobin majalisar ya amince da zaɓin kafin babban Sakataren ya iya kama aiki a muƙaminsa.