1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwalambiya: Babban taron siyasa na kungiyar FARC

Salissou Boukari MNA
August 28, 2017

'Yan kungiyar FARC da suka shafe shekaru fiye da 50 suna tawaye, sun rikide ga mayar da kungiyar ta siyasa, inda suke gudanar da babban taronsu na farko na siyasa.

https://p.dw.com/p/2iw8V
Kolumbien Farc-Guerilla beginnt Kongress zur Parteigründung
Babban zaman taron siyasa na FARC a birnin Bogota.Hoto: Reuters/J. Saldarriaga

An dai samu halartar wakillai 1200 da suka fito daga sassa dabam-dabam na kasar, inda za su yi nazarin hanyoyin da jam'iyyar ta su za ta dauka domin gwagwarmaya ta siyasa kamar yadda shugabansu Rodrigo Londoño ya sanar yayin buda babban zaman taron.

"Daga wannan lokaci, mun rikida mun koma sabuwar kungiya ta siyasa, wadda za ta rika gudanar da ayyukanta cikin doka da oda. Muna da tarin kalubale a gabanmu da kuma tarin wahalhalu, don haka harkokin siyasa ba abu ne masu sauki ba."

Tsawon kwanaki shida ne dai kungiyar ta FARC za ta shafe tana wannan babban zaman taro na siyasa bayan da a ranar 15 ga watan Agusta da ya gabata suka kammala ajiye makammansu na yaki. Shugaban kungiyar ya kara da cewa za su ci gaba da kokowa ta demokuradiyya da ke tabbatar da zaman lafiya da 'yancin jama'a a kasar.