Kuskuren tura wasikun korar ′yan EU a Birtaniya | Labarai | DW | 23.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kuskuren tura wasikun korar 'yan EU a Birtaniya

An dai soki lamirin ofishin cikin gidan da tabka wannan kuskure, da ka iya sanya fargaba a zukatan 'yan EU kimanin miliyan 3.2 da ke zaune a Birtaniya.

UK | Theresa May (picture alliance/AP Photo/M. Dunham)

Firaministan Birtaniya Theresa May

Ofishin kula da harkokin cikin gidan kasar Biratniya ya ce ya aike da wasiku kimanin 100 bisa kuskure ga 'yan kasashen tarayyar Turai inda ya gargade su cewa suna iya fuskantar dauri ko kora da karfin tuwo daga kasar.

A martanin da ta mayar dangane da wannan kataborar, Firaministan Birtaniya Theresa May ta nuna takaicinta bisa wannan kuskure.

Ta ce: "Wannan kuskure abin takaici ne da ofishin cikin gida ya tabka. Amma na samu labarin cewa sun gaggauta daukar matakin tuntubar mutanen da aka aike wa wasikun don ba su tabbacin cewa ba za a kore su daga Birtaniya ba. Ina mai tabbatar wa dukkan 'yan tarayyar Turai da ke Birtaniya cewa ba bu canji dangane da 'yancinsu da kuma matsayinsu na zama a Birtaniya."

An dai soki lamirin ofishin cikin gidan da tabka wannan kuskure, da ka iya sanya fargaba a zukatan 'yan EU kimanin miliyan 3.2 da ke zaune a Birtaniya. Da ma dai suna cikin zaman zullumi game da makomarsu bayan an kammala shirin ficewar Birtaniya daga EU.