Kuri′ar raba gardama a Birtaniya | Siyasa | DW | 23.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kuri'ar raba gardama a Birtaniya

A wannan Alhamis ce al'ummar Birtaniya suka fita zabe a wata kada kuri'ar raba gardama na ci gaba da zama ko ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai.

Ko yaya za ta kaya dai, wannan kuri'a za ta rubuta wannan tarihi domin za ta canja al'amura a cikin kungiyar ta EU.Ra'ayi dai ya zo daya cewar matukar kasar ta Birtaniya ta fice daga Kungyiar Tarayyar Turai EU to hakan zai yi matukar girgiza harsashen da kungiyar ta kafu akai, kana kuma wannan mataki zai kawo karshen rayuwar siyasa ta Firaministan Birtaniyar David Cameron. Saboda haka ne ma ya yi ta kokarin shawo kan al'ummar kasar da su ki ficewa daga kungiyar EU.

Ya ce: "Mun fi karfi, mun fi samun ingantuwar rayuwa mun kuma fi samun kwanciyar hankali a cikin Kungiyar Tarayyar Turai. A saboda haka ya zama wajibi mu zabi ci gaba da zama cikin kungiyar. Idan da akwai wani darasin da na koya a cikiin shekaru shida a matsayin Firaminista, shi ne tattalin arzikinmu ya fim komkai muhimmanci."

Tattalin arzikin Birtaniya zai fuskanci koma baya idan ta fita daga EU inji Firaministan, domin za a fuskanci karancin aikin yi da karancin kudin ga iyalai a Birtaniya.To sai dai su ma masu adawa da zaman kasar cikin dangin na Tarayyar Turai sun tashi haikann wajen neman karin goyon baya. Jagoransu kuma tsohon magajin garin birnin London Boris Johnson jawo hankali ya yi game da nuna kishin kasa na 'yan Birtaniya.

Ya ce: "Mun kai mataki na karshe, za mu tabbatar mun samu kowace kuri'a. al'ummar kasar nan na da zabi na tarihib da za su yi. A gani na za mu zabi ficewa. Hakika akwai batutuwa masu muhimmanci, amma kudi mai yawa ba shi ne muhimmi ba. Sake samun iko da tsarin shige da ficenmu da demokradiyyarmu suna da muhimmanci."

Shugabannin Turai dai sun yi ta jaddada muhimmancin Birtaniya a cikin kungiyar, saboda haka suka yi fatan za ta ci gaba da zama cikin dangi, inji shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

Ta ce: "Kamar yadda na sha fada, kuma zan maimaita, ina fata Birtaniya za ta ci gaba da zama cikin EU, ko da yake wannan zabi na hannun al'ummar kasar. Abin da muka magana tare shi ne cewaR za mu hada karfi da karfe don samar da wata Tarayyar Turai mai karfi."

Shi kuwa a nasa bangaren shugaban hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker jawo hankalin 'yan Birtaniyar ya yi da su san cewaR ba watab sabuwar tattaunawa da su.

Ya ce: "Mun kammala yarjejeniya da Firaminista Cameron. Ya samu iya yawan rangwame da a bangarenmu muka iya bayarwa. Saboda haka ba za a sake yin wata tattunawa ba ko canja wani abu a cikin yarjejeniyar da muka cimma da shi a watan Fabrairu ko a wasu kudurori da sjka shafi tattaunawar. In sun fice to sun fice ke nan bakin alkalami ya bushe."

Bisan ga dukkan alamu wadanda ba su yanke shawarar bangaren da za su jefa wa kuri'a ba, su ne za su tabbatar da wanda zai samu nasara a kuri'ar raba gardama da za ta fayyace makomarsu da ta Firaminista David Cameron da sauran ta Turawa.