1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kuntatawa 'yan adawa a Nijar

February 25, 2014

A Jamhuriyar Nijar 'yan jarida da masu adawa da gwamnati na fiskantar takurawa daga hukumomi, inda yanzu haka ake ci-gaba da shari'u da suka shafi 'yan jarida da masu adawa.

https://p.dw.com/p/1BFHu
Mahamane Ousman Ex-Präsident Niger
Mahamane OusmanHoto: DW/M. Kanta

Shari'ar fako dai ta shafi Alhaji Dudu Rahama kakakin jam'iyyar adawa ta CDS Rahama da kuma kungiyar kawancen jam'iyyun adawa na kasar ARDR. Shi dai wannan dan siyasa gwamnatin kasar na zargi shi ne da yi wa shugaban kasar kazafi bayan da ya zarge shi da bayar da cin hanci. Alhaji Dudu Rahaman ya bayyan haka ne a lokacin wani shirin mahawara mai farin jini da ya halarta a tsakiyar watan Janairun da ya gabata a gidan rediyo da talabijin na Bonferey mai zaman kansa da ke a kasar ta Nijar. Dama dai sai da ya share zaman gidan 'yan sanda na tsawon yini biyu a karshen watan na Janairu, ana yi masa tambayoyi kan wanann batu kafin daga bisani babban alkalin gwamnatin ya yi masa sakin wucan gadi tare da umartarsa da ya kasance a shirye domin karba kiran kotu wadda za ta ci gaba da zurfafa bincike a kan batu.

Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Mahamadou IssoufouHoto: DW/M. Kanta

A loakcin wanann zama na farko lauyan Alhaji Dudu Rahaman ya tsaya ne kai da fata wajen nuna rashin halarcin gudanar da wannan shari'a bisa zargin babban alkalin gwamnatin da tabka kura-kurai wajen tsara takardaun shigar da kara, kamar yadda ya shaida wa manema labarai jim kadan bayan fitowa daga zaman shari'ar:

"Akwai wa'adin da ya kamata in kamar mai shigar da kara ya bada sammashi bisa laifi na yin wata magana, a wani gidan rediyo ko talabijin to sai an baka kwana 15 dan ka shiryawa, amma idan ba a baka wannan lokacin ba, to shari'a ba ta tabbata ba, za a rushe ta. Dangane da zargin shugaban kasa da ba da cin hanci kai dan jarida ka sani kafin wani ya ji, a gurin 'yan jarida aka ji suna fadin haka kuma Alhaji Dudu Rahama shi ma ya maimata sai kuma a ce ya yi laifi. Kuma ma ba shi ya cancanta a kai kara ba domin duk mutummin da aka gayyata a talabijin ko rediyo a cikin wata mahawara ko rahoto. In ya yi magana ta kuskure wanda ake neman shi ne shugabannin gidan wanann rediyo ko talabijin sai in ba a same su ba ne, ake iya tuhumar mutumin"

Shari'a ta biyu ta shafi wani dan jarida ne Malam Usmane Dambaji
daraktan jaridar L'Union mai zaman kanta, da ke a kasar ta Nijar, shi kuma gwamnatin tana zarginsa ne da yi wa shugaban kasar kasafi a cikin wani shirin mahawara na harshen Hausa da ke gudana a gidan rediyo da talabijin "Canal 3" mai zaman kansa da ke a birnin na Yamai. Shi dai wanann dan jarida ya ambato cewa shugaban kasar ta Jamhuriyar Nijar Alhaji Mouhamadou Issoufou, a lokacin da ya ke yakin neman zaben kujerar shugaban kasa, ya yi wa wata mata a wani kauye alkawarin gina masu rijiya da zaran ya yi nasarar hawa kujerar mulki, amma kuma ya hau mulkin ba tare da cika wannan alkawari ba. Shi ma dai lauyan nasa Maitre Lirwana Abdurahmane, a lokacin wannan zaman shari'a ya dage ne a kan nuna rashin halarcin zaman shari'ar da kanta, a bisa hujjar kura-kurai da ya ce babban alkalin gwamnatin ya tabka wajan hada takardun karar. Inda ya yi karin bayani yana mai cewa.

DW im Niger Yahouza Sadissou Mabobi
Yahouza Sadissou Mabobi, ministan sadarwan NijarHoto: DW/M. Kanta

"Mu ka ce Alkali mai zargi ba ya da yancin ya yi ma Dambaji wannan zargin da ya yi mi shi, tun da laifin da ake zarginsa da shi ba laifi bane, wanda ya shafi maganar kabilanci ko addini, wanda alkali mai zargi na iya tuhumar mutun da kan shi, ko ba karan da wani ya shigar. A nan magana ce aka yi aka ce shugaban kasa lokacin da ya ke yakin neman zabi ya yi alkawari a wani gari zai yi rijiya, kuma ba a yi wanann rijiya ba, to kuma wanann zai zamanto laifi. To ai tun kafin ya zamo shugaban kasa ya fadi wannan magana, kuma shi shugaban kasa mutun ne dan Adam da kan shi ake jin an yi ma wannan zargi. Kenan shi ne da ya kamata ya shigar da kara, ba wai procureur din ba babban alkalin gwamnatin ba."

Alkalin da ke shari'ar ya tsaida ranar hudu ga watan Maris din gobe, domin bayyana matsayinsa a kan cancatar ci gaba da gudanar da wanann shari'a, ko kuma akasin haka.


Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Usman Shehu Usman