Kungiyyar Au zata aike da tawaga izuwa Chad | Labarai | DW | 20.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyyar Au zata aike da tawaga izuwa Chad

Kungiyyar hadin kann kasashen Africa, wato Au tace nan ba da dadewa ba zata aike da wata tawaga izuwa kasar Chadi don warware rikicin dake tsakanin su da Sudan.

Tawagar ta mutane shidda, a cewar kungiyyar ta Au zata bar birnin Addis Ababa a gobe juma´a ne izuwa kasar ta Chadi.

Kungiyyar ta Au ta kara da cewa, bayan duba yiwuwar warware rikicin dake tsakanin kasashen biyu, tawagar za kuma ta duba hali na kaka ni kayin siyasa da kasar ta Chadi ta fada a ciki , sakamakon rikicin yan tawaye da zummar samo bakin zaren.

Wannan rikici dai ya biyo bayan zargi ne da mahukuntan na Chadi suka yiwa Sudan da cewa suna daurewa yan tawayen kasar gindi, wajen cin karen su babu babbaka a kasar.

A dai yan kwanaki kadan da suka gabata ne, shugaba Idiris Debby na Chadi ya katse duk wata dangantaka ta diplomasiyya da kasar ta Sudan, bisa wannan zargi , koda yake ya zuwa yanzu tuni mahukuntan na Sudan suka musanta wannan zargi da cewa bashi da tushe balle makama.