1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kame wasu jiragen ruwan kasar Ukraine

Zulaiha Abubakar
November 26, 2018

Rahotanni daga Moscow sun bayyana yadda sojojin Rasha suka bude wa wasu jiragen ruwa na yaki mallakar kasar Ukraine wuta, yayin da suke kan hanyar su ta  ketarawa mashigin ruwan Kerch da ke yankin Crimea.

https://p.dw.com/p/38ta3
Russland Krim | Russische Kampofjets an der Straße von Kertsch
Hoto: Reuters/P. Rebrov

Ma'aikatar tsaron kasar Ukraine ta bayyana cewar wasu daga cikin jami'an tsaron kasar da ke cikin jiragen ruwan sun samu munanan raunuka sakamakon wannan hari. A baya gwamnatin Ukraine ta zargi Rasha da kai wa wani  jirgin ruwan ta hari a  yankin Azov,da  take maida martani ma'aikatar tsaron kasar Rasha, ta bayyana cewar tana da hujjoji game da yadda Ukraine ta ke amfani da jiragen yakin ta na ruwa, don neman kulla sabon rikici tsakanin kasashen biyu, wannan dalili ne ya sanya ta kame jiragen ruwa har guda uku na Ukraine .

Tuni dai kakakin kungiyar tsaro ta NATO ta yi kira ga kasar ta Rasha kan ta mutunta dokar walwalar jiragen ruwan Ukraine. A yau ne dai ake saran za'a yi zaman gaggawa na kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya kan wannan tashin hankali da ya barke tsakanin kasashen biyu.