Kungiyar OIC ta zargi Isra′ila da laifukan yaƙi | Labarai | DW | 12.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar OIC ta zargi Isra'ila da laifukan yaƙi

Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa ta OIC ta zargi Isra'ila da aikata laifukan yaƙi a Gaza sakamakon ruwan bama-baman da ta yi.

A wani zaman taro da ta gudanar a ƙasar Saudiyya wanda kuma shi ne na biyu a kan batun na Gaza, Ƙungiyar ta zargi Isara'ilan da ci gaba da kashe Falasɗinawa.

Sannan kuma ta yin kira wani zaman taro na ƙasashen duniyar musulmi domin samar da kuɗaɗen taimaka wa al'ummar Gaza. Tuni dai da Masar tac e za ta shirya zaman taron masu ba da gudunmowar don sake gina Zirin Gaza.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahamane Hassane