Kungiyar OEA ta ce za ta sa ido a zabukan kasar Haiti | Labarai | DW | 17.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar OEA ta ce za ta sa ido a zabukan kasar Haiti

Kungiyar kasashen yankin Amirka ta OEA ta sanar da aniyarta saka ido ga zabukan kasar Haiti wadanda za su gudana a watannin Agusta, da Oktoba da kuma Disamba na 2015.

Luis Almagro

Luis Almagro

Sakataran wannan kungiya Luis Almagro ne ya sanar da hakan, inda ya ce matakin da kungiyar ta kasashen yankin Amirka ta dauka na nuni da irin mahimmancin samar da kyakkyawar demokradiyya a kasar ta Haiti a zabukan da za su gudana. Sakataran kungiyar ta OEA ta kasashen Amirka ya kara da cewa, kungiyar za ta ba da tabbaci a yayin kidayar kuri'u wanda shi ne gimshiki na demokradiyya.

Za a nemi gurabe fiye da dubu shida da suka hada da shugabannin kananan hukumomi da kansiloli, 'yan majalisu da kuma shugaban kasa a ranar 09 ga watan Agusta, da ranar 25 ga watan Oktoba sai kuma ranar 27 ga watan Disamba.