Kungiyar Likitoci ta MSF ta soki kasashen duniya kan Ebola | Labarai | DW | 03.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Likitoci ta MSF ta soki kasashen duniya kan Ebola

Shugaba Obama na Amirka ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta sake amincewa a bada dalar Amirka miliyan dubu shida a matsayin tallafin gaggawa don yaki da wannan annoba.

Logo Médecins Sans Frontières Ärzte ohne Grenzen Kalenderblatt

Kungiyoyin agaji na likitoci da kungiyar likitoci ta nagari na kowa ta (Médecins Sans Frontières) sun yi kakkausar suka kan yadda kasashen duniya ke bada kulawa a yaki da ake yi da cutar Ebola a yammacin Afrika.

Kungiyar ta MSF ta ce ana samun tafiyar hawainiya kan yadda ake kai tallafi, inda aka bar aikin ga likitoci da ma'aikatan jiya da kungiyoyin agaji su ke ta fama a wannan fafutukar yaki da cutar ta Ebola.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa fiye da mutane 6000 suka rasu ta sanadin wannan cuta ta Ebola a cikin wannan shekara, mafi akasari a Laberiya, Saliyo da Guinea.

Shugaba Obama na Amirka ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta sake amincewa a bada dalar Amirka miliyan dubu shida a matsayin tallafin gaggawa dan yaki da wannan annoba ta Ebola.

Shugaban ya ce babu yadda za a yaki Ebola ba tare da karin kashe kudade ba.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu