Kungiyar kasashen Musulmi OIC tayi kira ga dakatar da zubda jini a Iraqi | Labarai | DW | 25.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar kasashen Musulmi OIC tayi kira ga dakatar da zubda jini a Iraqi

A halin da ake ciki kuma kungiyar kasashen musulmi ta duniya tayi kira da dakatar da zubda jini tsakanin yan sunni da yan shia a Iraqi,tana mai tunatarwa shugabannin addini na kasar alkawura da suka dauka na hana zubda jinin musulmi.

A daya hannun kuma wani jamiin kungiyar kasashen larabawa a birnin Alkhahira yace ana sa ran ministocin kasashen wajen kungiyar mai membobi 22 zasu gana a birnin Alkhahira a ranar 5 ga watan disamba inda zasu yi kira ga bangarorin dake yaki da juna a Iraqi dasu kawo karshen yawan zubda jini a kasar.

Sakataren kungiyar kasashen musulmi Ekmaleddin Ihsanoglu yace ya kamata shugabbanin addini na Iraqi wadanda sukayi rantsuwa a dakin Kaaba ba zasu zubda jinin yan uwansu musulmi da suji tsaron Allah su dakatar da wannan balai.

A dai ranar 20 ga watan oktoba ne shugabanin addinin na Iraqi sukayi kira ga magoya bayansu da su dakatar da fada tsakaninsu.