1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar kare hakki ta zargi Kenya

August 28, 2017

Kungiyar kare hakkin jama'a ta Human Rights Watch, ta zargi 'yan sandan kasar Kenya ta take hakkin jama'a bayan sanar da sakamakon zaben kasar da aka yi a farkon wannan wata na Agusta.

https://p.dw.com/p/2iyWc
Kenia nach Wahlen Unruhen und Protest
Jami'an tsaron KenyaHoto: Reuters/T. Mukoya

Kungiyar kare hakkin jama'a ta Human Rights Watch, ta zargi 'yan sandan kasar Kenya ta take hakkin jama'a bayan sanar da sakamakon zaben kasar da aka yi na ranar 8 ga wannan watan na Agusta. Akalla mutane 12 ne aka ne suka mutu a hargitsin ciki har da wani jariri dan wata shida da haihuwa.

Akwai ma wasu sama da mutum 100 da suka ji rauni sakamakon dukar da aka ce jami'an 'yan sanda suka yi masu. Masu adawa da nasarar shugaba Uhuru Kenyatta na kasar, sun tayar da bore ne jim kadan bayan bayyana rashin gamsuwa da sakamako da jagoran adawa Raila Odinga  ya yi, inda suka yi ta tayar da jijiyoyin wuya a Nairobi da ma wasu manyan birane na kasar.