Kungiyar Is ta nada sabon shugaba | Labarai | DW | 31.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Is ta nada sabon shugaba

Kungiyar IS ta sanar da nadin Abu Ibrahim al-Hashemi al-Qurashi dan asalin kasar Saudiyya a matsayin sabon shugabanta don maye gurbin tsohon shugaban Abu Bakr al-Baghdadi.

Baya ga sabon shugaba da kungiyar ta sanar da nadawa, har wa yau ta bayyana cewa an nada Abu Hamza al-Qurayshi a matsayin kakakinta wanda shi ne zai maye gurbin tsohon kakakin wato Abu al-Hasan al-Muhajir wanda aka kashe a wani hari na daban.

A ranar Lahadin da ta gabata ne shugaba Donald Trump na Amirka ya tabbatar da cewa harin sojin kasar ya halaka jagoran na kungiyar IS wadda ke fafutuka wajen kafa daular Islama a wasu sassan yankin Gabas ta Tsakiya.