Kungiyar Hamas ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da ka da ta katse kudaden taimakon da take bai wa Hukumar Falasdinawa. | Labarai | DW | 30.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Hamas ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da ka da ta katse kudaden taimakon da take bai wa Hukumar Falasdinawa.

Kungiyar nan ta Hamas, wadda ta lashe zaben Falasdinawa da aka gudanar a makon da ya gabata, ta yi kira ga gamayyar kasa da kasa da ka da ta dakatad da ba da taimako ga Hukumar Falasdinawan. Da yake jawabi a wani taron maneman labarai a zirin Gaza, daya daga cikin shugabannin kungiyar, Ismail Haniyeh, ya bukaci duk masu bai wa Hukumar Falasdinawan taimako da su ci gaba da tallafin da suke bayarwa. Ismael Haniyeh ya yi jawabin ne sa’o’i kadan kafin rukunin nan na masu shiga tsakani guda 4, wanda ya kunshi Amirka, da kungiyar Hadin Kan Turai, da Majalisar Dinkin Duniya da kuma Rasha, ya yi taronsa don tattauna sabon halin da aka shiga ciki a yankunan Falasdinawan, bayan gagarumar nasarar da kungiyar Hamas din ta samu a zaben da aka gudanar a makon da ya gabata.

Shugaban kungiyar dai ya yi watsi da damuwar da wasu bangarori ke nunawa, ta cewa Hamas za ta yi amfani da tallafin da take samu ne wajen ta da zaune tsaye a yankin. Ya tabbatar wa gamayyar kasa da kasar cewa, duk wasu kudaden taimako da za su shigo hannun Hukumar Falasdinawan, za a yi amfani da su ne wajen biyan albashin ma’aikata, da gyara gine-gine da kuma inganta halinn rayuwar jama’a na yau da kullum. Ya kuma ce a shirye Hamas din take ta yi shawarwari da rukunin a kan duk wasu batutuwan da za su taso.