Kungiyar EU za ta tallafa wa bakin haure | Labarai | DW | 20.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar EU za ta tallafa wa bakin haure

Rasuwar daruruwan bakin hauren Afirka a teku ya sa gwamantocin kasashen Turai sun yin yunkurin canja kamun ludayinsu dangane da ayyukan cetonsu daga mawuyacin hali.

Taron ministocin harkokin wajen kasashen Turai da suka fara a ranar Litinin nan ya amince cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an tsaida rasuwar mutane barkatai da ke hallaka a tekun Bahar Rum inda za su fadada ayyukan ceto da kama masu fasakaurin al'umma. Wannan mataki kuma na zuwa ne bayan karuwar rasuwar mutane 700 a karshen makon da ya gabata bayan sun baro gabar teku daga kasar Libya.

Da yawa daga cikin gwamnatocin kasashen Turai sun ja da baya wajen daukar nauyin ayyukan ceto a tekun na Bahar Rum a matsayin gargadi da sanyaya gwiwa ga jama'ar da ke son kwarara zuwa kasashen na Turai don neman ingantar rayuwa. Sai dai mutuwar bakin ta sanya kasashen sauya tunani. Abinda ya sanya ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ke ganin cewa ya zama dole a duba lamarin duk da irin matsalolin da ke gaban kasashen na Turai.

"Muna fama da tarin matsaloli kuma ina son na dan yi jan hankali anan cewa ba za a sami waraka daga wannan matsala cikin sauki ba sai dai ya zama wajibi a garemu mu tausaya ga iyalan matatan kuma mu gaggauta ganin cewa ba a ci gaba da samun wadanda ke rasa rayukansu a cikin tekun na Meditareniya ba cikin gaggawa".