Kungiyar EU ta sanar da ba da agajin gaggawa ga Indonesia | Labarai | DW | 27.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar EU ta sanar da ba da agajin gaggawa ga Indonesia

Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai ta ce zata bawa Indonesia agajin gaggawa na Euro miliyan 3 don taimakawa wadanda mummunar girgizar kasar ta rutsa da su. Wannan girgizar kasar wadda ta halaka akalla mutane dubu 2 da 700 sannan ta jikata dubbai ita ce wani bala´i mafi muni da ta afkawa kasar tun bayan igiyar ruwan tsunami a karshen shekara ta 2004. Kwamishinan raya kasashe na KTT Louis Michel ya ce nan da sa´o´i kalilan masu zuwa suna sa ran cewa kungiyar ba da agaji ta kasa da kasa wato Red Cross da kuma kungyiar Red Crescent zasu ba gabatar da wani roko na farko a saboda haka hukumar EU ta shirya don ba da taimakon gaggawa da nufin kawo saukin halin da ake ciki. Hakazalika gwamnatocin kasashen EU na cikin shirin tura kayan aiki da ma´aikatan ceto zuwa yankin da girgizar kasar ta afka ma, inji Michel.