1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar EU ta nemi hadin kan Turai bayan zabe

May 26, 2014

Magabatan na Turai dai sun yi mamakin sakamakon zaben 'yan majalisar, sai dai acewarsu sun amince da shi, kana akwai bukatar inganta ci gaban nahiyar.

https://p.dw.com/p/1C7IK
Jean-Claude Juncker Martin Schulz Spitzenkandidaten Europawahl
Hoto: Getty Images

Masu kada kuri'u a Nahiyar Turai sun bayyana ra'ayinsu ta irin kuri'u da suka kada a tsawon kwanaki hudu na zaben 'yan majalisa a tsakanin kasashe 28 masu wakilci a EU, inda sakamakon ya kasance mai razanarwa ga magabatan kungiyar, ganin cewar jam'iyyun da ke muradin sauyi ne suka samu galaba.

Ana yi wa sakamakon zaben na 'yan majalisar Turai kallon mai adawa kai tsaye da manufofin 'yan siyasar nahiyar, wanda ke tabbatar da cewar za'a samu matsala idan mahawara ta taso danmgane da batutuwa da dama, da suka hadar da sakarwa harkokin kasuwanci na cikin gida mara, wadanne abubuwa ya dace ayi la'akari da su a tsarin yarjejeniyar kasuwanci da Amurka, har da kuma yadda za'a cimma daidaito a fannoni daban daban da ake samun makamashi.

Sanarwar da ya gabatar a wannan litinin, shugaban hukumar gudanarwar Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso, na nuni da cewar majalisar gudanarwar kungiyar ta amince da sakamakon zaben. Ya ce wannan lokaci ne na hadin kai domin samarwa kungiyar kyakkyawar makoma, domin za'a iya cimma warware damuwar wadanda suka jefa kuri'u cikin korafi dama wadanda suka ki jefa kuri'unsu ne, ta hanyar daukar matakan siyasa da suka cancanta in samar da ci gaba da ayyuka, ta kyawawan hanyoyi na sahihin demokradiyya.

SPD Martin Schulz Empfang in Berlin 25.05.2014
Schulz 'yan jam'iyyarsa ta SPDHoto: Reuters

Gwagwarmayar shugabancin hukumar Tarayyar Turai da ke zama mafi girman kujera a nahiya dai, ya fara tun da safiyar wannan Litinin, inda tsohon fraiministan Luxemburg kuma dan takara Jean-Claude Junker ya ce a shirye yake ya karbi shugabancin hukumar.

" Mun samu galaba a wannan zabe.... kuma a ganina ni ne na cancanci kasancewa shugaban hukumar gudanarwar Turai".

Duk da wannan nasara da yake ikirari dai ya zama wajibi shugabannin gwamnatoci EU 28 su zabe shi, wadanda ke ganawa ranar talata da maraice domin tattauna zaben, kuma majalisa ce zata yi amana da nadin nasu.

A bokin takararsa na jam'iyyar socilaist Martin Schulz shima ya ayyana cewar, zai yi kokarin samun goyon baya ga wannan takara tasa: " Da ni da abokin takarata Jean-Claude Junker, muna neman kuri'u masu rinjaye, amma dole mu tattauna da juna. Akan ko zamu iya aiki tare, wanda hakan zai bayyana a kwanaki masu gabatowa. Amma dole ne ya kasance ko Juncker ko Schulz".

EU Parlamentswahl 25.05.2014 Deutschland SPD Schulz Berlin
Lokacin zabeHoto: Reuters

A taron manema labaru data gudanar a Berlin, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, bayyana mamaki ta yi da kuma nuna takaici dangane da irin karfin da wasu jam'iyu masu ra'ayin kawo sauyi ke dashi a zaben na 'yan majalisar Turai.

Fraiminista Manual Valls na jam'iyar socialist a Faransa, ya bayyana a gidan talabijin na kasar yana mai cewar, sakamakon zaben na nunar da cewar yana da matukar muhimmanci gawamnatinsa ta tursasa batun rage kudaden da ake kashewa da kuma haraji, da ta jima tana alkawrin aiwatarwa.

A yanzu haka dai babu bangarorin da ke da isassun kuri'u na rinjaye kai tsaye tsakanin masu ra'ayin rikau da masu neman sauyi. Sai dai a cewar Juncker Schulz, jam'iyyu siyasa zasu yi hadaka, a maimakon a bi lissafi wajen tabbatar da hakan.

Ana iya sauraron sauti daga kasa

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal