Kungiyar AU zata tattauna game da batun mika Habre ga kasar Belgium | Labarai | DW | 26.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar AU zata tattauna game da batun mika Habre ga kasar Belgium

Shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya zai mika batun tsohon shugaban kama karyar Chadi Hissene Habre a gaban taron kolin da kungiyar tarayyar Afirka zata yi a cikin watan janeru. An jiyo haka ne daga bakin mai magana da yawun shugaban na Nijeriya, Remi Oyo lokacin da ta ke magana da kamfanin dillancin labarun AFP. A yau asabar ´yan sanda sun sake kame Hisseni Habre kwana daya bayan sakin da wata kotu ta yi bayan ta kasa yanke hukuncin game da mika shi ga hukumomin kasar Belgium. Chief Obasanjo wanda shi ne shugaban kungiyar AU kuma yanzu haka yake halartar taron kolin kungiyar Commonwealth ta kasashe 53 renon Ingila a Malta, ya tattauna da shugaban Senegal Abdoulaye Wade akan wannan batu inji Misis Remi Oyo. Kasar Belgium dai na neman Habre akan zargin da ake yi na aikata ta´asa a zamanin mulkin sa daga 1982 zuwa 1990. Tun bayan hambarad da shi yake zaune a Senegal.