1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar AU ta dakatar da Burkina Faso

January 31, 2022

Kungiyar Tarayyar Afirka ta ce ta dakatar da kasar Burkina Faso daga kungiyar biyo bayan juyin mulkin da dakarun soji suka yi a ranar 24 ga watan Janairun nan.

https://p.dw.com/p/46Jsv
 Paul-Henri Sandaogo Damiba | Jagoran juyin mulki a Burkina Faso
Hoto: Facebook/Präsidentschaft von Burkina Faso

A sakon da kungiyar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce ta dakatar da kasar daga kungiyar har sai an mayar da ita tafarkin dimokaradiyya. Shugaban Majalisar gudanarwar kungiyar Moussa Faki Mahamat tuni ya yi tir da juyin mulkin.

Ita ma Kungiyar Yammacin nahiyar Afirka ECOWAS ta dakatar da Burkina Faso daga kungiyar a ranar Juma'ar da ta gabata tare da turawa da tawaga don ganawa da majalisar mulkin soji a kasar a karshen mako.

Kasar Burkina Faso dai ta sha fama da matsalolin tsaro tun bayan samun 'yancin kanta daga Faransa a shekarar 1960.