Kungiyar AU na shirin dakatar da Masar | Labarai | DW | 05.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar AU na shirin dakatar da Masar

Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU ta ce ta na duba yiwuwar dakatar da kasar Masar bayan da soji su ka kawar da gwamantin shugaba Muhammad Mursi daga gadon mulki.

Das Emblem der Afrikanischen Union befand sich auch in der Mitte der vorhergehenden Flagge der Afrikanischen Union. Quelle: Wikipedia Diese Datei stellt ein Amtliches Werk dar und ist nach § 5 UrhG (DE) bzw. § 7 UrhG (AT) und Art. 5 URG gemeinfrei.

Das Emblem der Afrikanischen Union

Majalisar tsaro da zaman lafiya ta kungiyar ta AU ta ce za ta tattauna kan wannan batu na yiwuwar dakatar da Masar din daga AU din ne a wannan Juma'ar yayin wani zama da za ta yi.

Da ta ke sharhi kan kifar da gwamnatin Mursi, shugabar kungiyar ta AU Nkosazana Dlamini-Zuma ta ce wannan wani mataki ne da kungiyar ba za ta lamunta ba inda ta kara da cewar hakan karen tsaye ne ga tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar.

A nasa bangaren shugaban majalisar tsaro da zaman lafiya ta kungiyar ta AU Ramtane Lamamra ya shaidawa kamfanin dillancin labarai Reuters cewa nan gaba kadan za su tura wata tawarsu zuwa kasar ta Masar domin neman tattaunawa da sojojin kasar don ganin an gudanar da wani zama da zai kai ga daidaita al'amura a kasar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu