1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Amnesty ta yaba wa Kamaru

August 31, 2017

Kungiyar kare hakkin jama'a ta Amnesty International ta yi marhabin da matakin da gwamnatin Kamaru ta dauka na soke zargen-zargen da ta ke yi wa wasu 'yan yankin kasar da take tsare da su.

https://p.dw.com/p/2j7rp
Amnesty international Logo
Hoto: picture-alliance/dpa/S.Kahnert

Kungiyar kare hakkin jama'a ta Amnesty International ta yi marhabin da matakin da gwamnatin Kamaru ta dauka na soke dukkanin zargen -zargen da ta ke yi wa wasu 'yan yankin kasar da ke amfanin da Ingilishi, wadanda da ma take tsare da su. Ita dai gwamnatin ta Kamaru ta tsare mutanen su biyu 'yan fafutika ne, saboda boren nuna rashin gamsuwa da abin da susa ce fifita harshen Faransanci sama da Ingilishi da ake yi a Kamarun.

Mutanen sun yi zaman watanni shida saboda zarginsu da aikata laifi mai nasaba da ta'addanci, bayan kiran yajin aiki da sunan neman kwato 'yancin yankin mai amfani da Ingilishin, da suka ce yana fama da wariya. Gwamnatin ta Kamaru, ta ce ta jingine maganar ne, don yayyafa wa batun ruwa. Kashi 20 cikin 100 na al'umar Kamarun ne dai ke amfani da turancin Ingilishi a kasar.