Kungiyar Amnesty International ta fitar da rahoto | Siyasa | DW | 24.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kungiyar Amnesty International ta fitar da rahoto

Bayan gudanar da bincike a tsakanin kasashe 160 a duniya kungiyar ta Amnesty ta ce akwai sabbin matsaloli na take hakkin dan Adam a kasashen duniya.

A kasashe da suka hada da na Afirka, muradu na Ajandar 2063 na kungiyar kasashen Afirka AU da shirin Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba me dorewa SDGS wasu ginshikai ne da za su sanya fata na cimma muradun kare hakkin bil Adama. To sai dai ga baki dayan shekarar ta 2015 an ga take hakkin dan Adam da ke zama mai muni a kasashe irinsu Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Sudan da Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango da Burundi haka batun yake idan aka dawo Kamaru da Chadi da Kenya da Mali da Najeriya da Nijar inda dubban al'umma suka rasu wasu ke zaune cikin yanayi na fargaba da tashin hankali a ciki da wajen kasashensu da suka je neman mafaka. kamar yadda Netsanet Bellay daraktan kula da sashin Afirka a kungiyar ta Amnesty International ke cewa:

"Miliyoyin al'umma a kasashen Afirka a shekarar 2015 sun ga tashin hankali, dubban fararen hula sun rasu wasu sun sami raunuka sakamakon ayyukan kungiyoyin tada kayar baya irinsu Boko Haram da Al-Shabab a Najeriya da Kamaru da Kenya da ma wasu yankunan. A Najeriya da Kamaru soja sun yi amfani da karfin da ya wuce kima wajen kame mutane da halaka wasu da ma sauran nau'o'i na take hakkin dan Adam."

A cewar rahoton na Amnesty International a Najeriya wadanda ake zargin ana ci gaba da garkame su koda kuwa kotu ta bada belin su alal misali har shekarar ta 2015 ta fita Nnamdi Kanu jagoran 'yan fafutikar 'yantar da yankin Biafra na garkame, ga sambo Dasuki tsohon mai bada shawara ga gwamnatin shugaba Jonathan saboda zargin badakala a kudaden siyen makaman yaki da Boko Haram, wacce a shekarar dakarun sojan kasar suka kubutar da mutane 1400 daga hannunsu. Su ma dai wadanda ake zargi da zama 'yan kungiyar ba a basu wata dama ta ganawa da iyalansu ba. A cewar wata kungiyar kare hakkin tsiraru wadanda ake zargi 'yan luwadi da madigo 200 sun sha duka a Najeriya, ga yadda 'yan Shi'a suka ga tasku da kisan ba gaira a kasar. Abin da ke faruwa a kasashe da dama na Afirka a cewar Bellay da ke sanya idanu a kasashen na Afirka a kungiyar ta Amnesty.

"Gwamnatoci da dama a Afirka kamar a Habasha da Eritriya da Gambiya da Angola, na ci gaba da take hakkin 'kungiyoyin 'yan fafutika da masu kare hakkin dan Adam kamar 'yan jarida da marubuta a taskar Blogg, Abin da suke fakewa da cewa suna kare al'umma da hana ayyukan ta'addanci su takaita ayyukansu."

A karshen shekarar ta 2015 dai a Jamhuriyar Nijar mutane 115,000 ne suka shiga kasar a matsayin 'yan gudun hijira musamman a yankin Diffa saboda rikici na Boko Haram a Najeriya da rikici a Libya da Mali, a cewar rahoton, yayin da mutane 100, 000 suka watsu cikin kasar. 'Yan adawa na fuskantar kame-kame a kasar suma sojan na Nijer an samesu da gallaza wa 'yan gudun hijira lokacin tilasta musu komawa Najeriya a lokacin da wasu ke neman zuwa kasar bayan tattaki mai tsawo daga Najeriya inda wasu ma a hanyar zuwa sansanin Nguigmi suka rasu. Abin da ke nuna bukatar shugabannin na Afirka su tashi tsaye dan tunkarar wannan kalubale a cewar Bellay.

"Shugabanninmu na Afirka ya kamata su maida hankali wajen bada kariya ga batutuwa da suka shafi kare hakkin dan Adam abin da ke ci gaba da zagayawa na zame wa nahiyar babban kalubale."

A cewar Bellay dai haki ne da ya rataya a wuyan dukkanin kungiyoyi da ke wakiltar yankunan nahiyar ta Afirka su tashi tsaye wajen kare hakin miliyoyin al'ummar yankin da ke fama da tasku, musamman ganin yadda suka kira shekarar nan ta 2016 a matsayin shekarar kare hakkin dan Adam.

 

 

Sauti da bidiyo akan labarin