Kungiyar al-Shabaab ta kai hari a Baidoa | Labarai | DW | 12.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar al-Shabaab ta kai hari a Baidoa

Soja daya da kuma 'ya'yan al-Shabbab uku suka rigamu gidan gaskiya a harin da kungiyar ta Kai gidan gwamnatin Baidoa a gabashin kasar Somaliya.

'Yan bindiga na kungiyar al-Shabaab da ke da kaifin kishin Islama sun kai hari a birnin Baidoa da ke gabashin Somaliya, a wata cibiya da ta kunshi fadar gwamnatin wannan yanki da kuma hedkwatar sojojin kiyaye zaman lafiya na Afirka da kuma na Majalisar Dinkin Duniya. wata kafa ta tsaro ta bayyana cewa soja daya dan asalin Habasha ya rasa ransa a wannan harin, yayin da 'yan bindiga uku suka gamu da ajalinsu lokacin da suka tayar da bam da ke daure a jikinsu.

'Yan kungiyar al-shabaab suka ce sun kai wannan harin ne da nufin tarwatsa taron da gwamnatin yankin Baidoa ya ke gudanarwa da rundunar kasa da kasa ta kiyaye zaman lafiya.Birnin Baidoa mai da nisan kilometa 220 da Mogadiscio ya taba zama tungar 'yan al-shabaab tsakanin shekaru 2009 zuwa 2011 kafin sojojin Habasha su yi nasarar mayar da shi karkashin kulawar rundunar kasa da kasa.