Kungiyar Abzinawan Mali ta MNLA,taki ta aje makamai | Labarai | DW | 10.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Abzinawan Mali ta MNLA,taki ta aje makamai

A wani matakin samo warware bakin zaren rikicin dake tsakanin abzinwan arewacin Mali da suka kafa kungiyar gwagwarmaya da ,ECOWAS ta bukaci tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin biyu

default

Mayakan MNLA

Kungiyar 'yan tawayen abzinawa ta MNLA ,tace sam baza ta ajiye makamai ba domin shiga tattaunawa da hukumomin kasar ta Mali.
A cikin wata sanarwa da magatarkadan kungiyar, Bilal Ag Acherif, ya karanta a jiya Asabar,kungiyar ta yi watsi da duk wata bukatar ajiye makamai kamun aikwa da wata tawaga ta musamman daga majalisar dinkin duniya a matakin shiga tattaunawa da hukumomin Bamako.
Dama dai tun can farko kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin afirka ta ECOWAS ko kuma CEDEAO ce ta kira bangarorin biyu da su shiga tattaunawar sulhu .
Kungiyar dai tace tana gwagwarmaya ne domin kwatowa abzinwan Azawak 'yanci daga cin zarafin da suke fuskanta daga sojojin gwamnatin na Mali,zargin da Bamako ta musanta.
Yayinda a dai hannun daya ake ci gaba da farautar mayakan kungiyoyin kishin addini a arewacain kasar inda suka ja daga a cikin tsaunikan Ifoghas kusa da kan iyaka da kasar Aljeriya.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi