1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kundin Tsarin Mulkin Libiya zai kawo sauyin da kasar ke bukata

April 14, 2014

A wannan Litini ne wata majalisar mashawarta a Libiya, ta fara zaman samar da kundin tsarin mulkin, da kasar ke bukata cikin gaggawa domin daidaita lamura da dama

https://p.dw.com/p/1Bhpc
Libyen Tripolis Blockade Ministerien 30.04.2013
Hoto: REUTERS/Ismail Zitouny

Ana sa ran wannan majalisar, za ta yi amfani da tsohon kundin tsarin mulkin kasar mai shekaru 63 a matsayin wani ginshikin cimma wannan buri, kuma hakan na zuwa ne yayin da lamarin tsaro a kasar ta Libiya ke cigaba da tabarbarewa, kuma a cikin wannan hali ne ake bukatar ganin an girka sabon kundin tsarin mulkin kasa.

A halin da ake ciki dai Libiya na bukatar abin da kowace kasa ke bukata idan tana so ta gudanar da mulki yadda ya kamata, wato ta samar da gwamnati, da shugaba, da kundin tsarin mulki, sannan ta tabbatar da tsaro da kuma daidaito a kasar.

Wannan majalisa dai tana da babban kalubale a gabanta, domin tun kafin ma a zabe su aka fara fiskantar matsaloli, sau biyu aka so yin zaben a watan Fabrairu amma sakamakon yawan barazanar 'yan tawaye, da fashewar bama-bamai, aka rufe ofisoshin zabe, kana kuma kabilun marasa rinjaye kamar Berber, da Abzinawa da Tebu suka kauracewa zaben domin kujeru biyu kadai aka basu a cikin kujeru 60.

Libyen Wahl Verfassungsgebende Versammlung
Da kyar zaben samun wakilai ya gudana sakamakon rashin tsaroHoto: Getty Images/AFP

Libiya na bukatar kundin tsarin mulkin da zai yi tasiri

Daga karshe dai kashi 14 cikin 100 na wadanda suka cancanci kada kuri'a suka fito suka yi zabe, shi ya sa da yawa ke shakkun cewa anya kundin tsarin mulkin da za a yi zai yi la'akari da bukatun 'yan kasa kuwa musamman irin banbance-banbancen da suke da shi? Wolfgang Pusztai kwararre ne kan tsaro wanda ke ganin duk yadda aka yi za a sami wani rukunin al'ummar da zai ce an kuntata mi shi.

"Ga Libiya abu na musamman shi ne ma a sami irin tsarin mulkin da kasar za ta yi amfani da shi, za ta dauki tsarin sarauta ne wanda ke amfani da kundin tsarin mulki? domin da yawa na fatan ganin hakan, za ta zama jamhuriyar Islama ne ko kuwa kasa mai gwamnatin tarayya? Ta yaya kuma za a rage karfin iko daga tsakiya domin da yawa ma na da wannan ra'ayi, kuma idan haka ne wace rawa manyan yankunan kasar guda uku za su taka?, kuma wace rawa ita ma addini za ta taka?"

Libyen Feier Jahrestag 3 Jahre ohne Gaddafi in Tripoli
Shekaru uku ke nan Libiya babu GaddafiHoto: Reuters

Me kasar Libiya ke bukata a zahiri?

A wannan litini ne kuma ake shari'ar 'ya'yan marigayi kanar Gadddafi Saif al-Isam da Saadi Gaddafi, wadanda ake zargi da kissa, da yin garkuwa da mutane da kuma yin sama da fadi da dukiyar kasa, amma duk ma me ake ciki a 'yan makonni masu zuwa, dole ne wakilan wannan majalisa su fayyace tsarin mulki, da ma irin tasirin da tsarin shari'a zai yi a bangaren shari'ar kasar, wanda idan har suka kammala, za su gabatarwa majalisar rikon kwaryar kasar kafin a yi zaben raba gardama, domin ganin ko zai sami karbuwa. Mouhamad Mahmoud Ould Mohamedu jami'i ne a wata cibiyar kula da manufofin tsaro dake birnin Geneva ya ce matsalar Libiya a yadda take yanzu, abin da take bukata ya fi karfin kundin tsarin mulki.

"Akwai wani yanayi na tarbarbarewar lamuran ikon dake faruwa a Libiya, kuma a waje na wannan ne babban labarin, saboda haka, kamata yayi a samar da kundin tsarin mulkin daura da daukan matakan gina kasa ta yadda za a yi la'akari da sabbin bukatu, yanzu a maimakon haka, ana siyasa ce ta tawaye domin an sami karuwar kungiyoyin tawaye wadanda ke da karfi sosai har ma su suke fadawa gwamnatotin da suka biyo bayan faduwar Gaddafi abin da suke gani ya fi mahimmanci ga kasar".

Abin jira a gani dai shi ne tsarin mulkin da majalisar za ta gabatar a matsayin wanda ya fi dacewa kafin a san inda kasar ta dosa.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Mohammed Awal Balarabe