Kuncin rayuwa a jihohin da aka kafa dokar ta-baci | Siyasa | DW | 27.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kuncin rayuwa a jihohin da aka kafa dokar ta-baci

Tun bayan da gwamnatin Najeriya ta kafa dokar ta-baci a jihohi uku na arewa maso gabacin kasar a watan Mayu, jama'ar yankin ke fama da matsalolin rayuwa iri-iri.

Hukumomin kasar ta Najeriya sun dauki wannan mataki ne don magance tashe-tashen hankula da kuma hare-haren da ake zargin 'ya'yan kungiyar nan da ake wa lakabi da Boko Haram da kaiwa a yankin na arewa maso gabacin kasar. Sai dai wannan mataki ya jefa jama'ar yankin cikin kuncin rayuwa.

DW.COM