Kudurin neman amincewa da kasar Falasdinu | Labarai | DW | 29.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kudurin neman amincewa da kasar Falasdinu

Kungiyar Hadin Kan Larabawa ta ce Jordan za ta mika sabon daftarin kudurin da zai samar da wa'adin girka kasar Falasdinu ga Kwamitin Sulhun MDD

Kasar Jordan wadda ta kasance mamba a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya daga yankin Larabawa za ta gabatar da wani daftarin kudurin da zai sanya wa'adin tsawon lokacin da za a dauka domin girka kasar Falsadinu, a nan da 'yan kawanaki masu zuwa. Shugaban Kungiyar Hadin-kan Larabawa Nabil Araby ne ya tabbatar da wani labari.

A cewar kamfanin dillancin labaran Reuters Babban jami'in kungiyar larabawan ya ce an dade ana kunbiya-kunbiya kan wannan bukata ta samar da kasar Falasdinu, amma abin da ya kasance sabo a wannan karon shi ne Falasdinu da kanta, ta yanke shawarar zuwa Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, da daftarin kudurin Larabawa ta hanyar kasar Jordan.