Kudirin Majalisar Dinkin Duniya kan Siriya | Labarai | DW | 28.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kudirin Majalisar Dinkin Duniya kan Siriya

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudirin ba da umurnin lalata makamai masu guba na kasar Siriya.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudirin ba da umurnin lalata makamai masu guba na kasar Siriya. Idan kasar ta ki bayar da hadin kai, za a gabatar da kudiri na biyu da zai bukaci amfani da karfin soja.

Da yammacin wannan Jumma'a da ta gabata aka amince da matakin, wanda ya zama karo na farko da aka samu matsaya cikin rikicin kasar na shekaru biyu da rabi. Kasashen Rasha da China sun dakile duk sauran yunkirin da ake yi na baya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya kira matakin da cewa fata mai kyau ta farko kan rikicin Siriya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh