Kuba: Guguwar Irma ta hallaka mutane 10 | Labarai | DW | 11.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kuba: Guguwar Irma ta hallaka mutane 10

Hukumomi a kasar Kuba sun ce akalla mutane 10 suka rasu biyo bayan mahaukaciyar guguwar nan ta Irma da ta afkawa wasu sassan na kasar. Wadanda suka rasu din dai na tsakanin shekaru 27 zuwa 89.

Baya ga wanda suka rasu, jami'an tsaro sun ce guguwar wadda ta isa kasar tun a ranar Asabar ta yi mummunan ta'adi ga gine-gine musamman ma a Havana babban birnin kasar. Wannan lamari dai ya sanya an kwashe kimanin mutane dubu 10 don ceton rayuwarsu. Daga cikin wannan adadi da aka kwashe har da 'yan kasashen waje da suka shiga kasar yawon bude idanu. Fitar wannan labari na zuwa ne daidai lokacin da hukumomi a Amirka ke cewar karfin guguwar Irma din musamman a jihar Florida ya fara raguwa kuma ana sa ran kara raguwasa a gobe Talata idan Allah ya kaimu.