1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kramp-Karrenbauer ta samo hanyar kare rikicin Siriya

Abdullahi Tanko Bala AAI
October 22, 2019

Ministar ta tsaron Jamus, ta bada shawarar hanyoyin da suka dace a bi wadanda suka sami karbuya gun jam'iyyun 'yan mazan jiya dan kawo karshen rikicin Siriya da ke cigaba da ruruwa.

https://p.dw.com/p/3RjWt
Ministar tsaron Jamus Annegret Kramp-Karrenbauer
Ministar tsaron Jamus Annegret Kramp-KarrenbauerHoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Ministar tsaron Jamus Annegret Kramp-Karrenbauer ta bada shawarar samar da tudun mun tsira a arewacin Siriya a wani mataki na kwantar da tarzoma a yankin da ma kuma kawo karshen rikicin da ke kara ruruwa a kasar. Ministar ta baiyana wannan bukata ce a wata hira da tashar DW. Shawarar wadda ministar tsaron ta Jamus Annegret Kramp-Karrenbauer za ta gabatarwa kasashe aminan Jamus a kungiyar kawancen tsaro ta NATO a Brussels a ranar Alhamis ya sami amincewa daga jam'iyyun 'yan mazan jiya. Bugu da kari kudirin zai baiwa Jamus da Kungiyar Tarayyar Turai damar tura sojoji zuwa yankin. Annergret ta ce sau da dama akan nuna cewa Jamus na kin sanya hannu a rikicin da ya shafi kasa da kasa tana mai cewa wannan babban abin jarumta ne kasar ta nuna. Ministar ta kara da cewa majalisar dokokin Jamus ita ce za ta yanke shawara ko ya dace a aike da rundunar sojin kasar zuwa yankin.

"Shawarar da na bayar ita ce mu samar da tudun mun tsira na kasa tare da goyon bayan kasashen Turkiyya da Rasha wadda ke zama babbar aminiyar shugaban Siriya Bashar al Assad. Wannan yanki na tsaro shi zai karbi ragamar yaki da 'yan ta'adda da kuma 'yan ISIS wanda aka daina a halin yanzu. Bugu da kari matakin zai tabbatar da cewa mun kawo zaman lafiya a yankin, yadda za a sami damar cigaba da gina rayuwar fararen hula inda ma wadanda suka yi kaura za su iya dawowa don radin kansu." Makonni biyu da suka gabta ne rundunar sojin Turkiyya ta kaddamar da farmaki kan mayakan Kurdawan yakin na Kungiyar YPG da nufin kwace yankin da ke hannunsu don mayar da shi wani sabon matsugunin miliyoyin 'yan Siriya da ke zaman gudun hijira a Turkiyya. 

Türkische Militäroffensive in Nordsyrien | Luftangriff in Ras al-Ain
Yadda ake barin wuta a yankunan SyriaHoto: AFP/D. Souleiman

Sai dai kuma a waje guda shawarar ta bar baya da kura inda jam'iyyar adawa ta SPD ta soki shawarar, tana mai cewa ba a tuntube ta ba kamar yadda Fritz Felgentreu na jam'iyyar ta SPD yake cewa:   

"Shugabanni a kwamitin kawancen hadaka sun shafe tsahon sa'o'i suna tattaunawa game da halin da ake ciki a arewacin Siriya kuma Ms Kramp-Karrenbauer ba ta yi kuskure ba a game da shawararta. To amma muna da namu shakku bai kuma shafi tambayar cewa mai yasa Rasha da Amirka za su janye a yanzu ba, su bar sojojin yammacin Turai a arewacin Siriya? 

Fritz Felgentreu shugaban kwamitin tsaro na Jam'iyyar SPD a majalisar dokoki a nasa ra'ayin ya yi bayani yana mai cewa:-

"Mun san cewa akwai matsala sosai a arewacin Siriya. Wajibi ne mu tunkare shi gaba daya. Kuma mun san cewa wannan yanki yana da wani abu da ya shafi tsaronmu a nahiyar Turai. Mun ga yadda 'yan IS suka jefa rayuwar mutane a Turai cikin babban hadari, a saboda haka ya zama wajibi mu shiga yaki da IS kamar yadda ake muhawara a nan Jamus cewa kasar na da rawar da za ta taka wajen kawo dai-dai-to da zaman lafiya a yankin. Sai dai kuma ya kamata a sami cikakken halacci na yin hakan."

Bashar al-Assad shugaban kasar Syria
Bashar al-Assad shugaban kasar SyriaHoto: picture-alliance/AP Photo/Facebook page of the Syrian Presidency

A makon da ya gabata shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bada shawarar gudanar da taron koli tsakanin kasashen Faransa da Birtaniya da kuma Turkiyya domin tattauna yadda za a kawo karshen tabarbarewar al'amuran tsaro a arewacin Siriya. Akalla fararen hula dubu 160 suka tagaiyara tun bayan farmakin da Turkiyya ta kaddamar a ranar 9 ga wannan watan Oktoba a cewar alkaluma na hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya.