1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bunkasar koyon harshen Jamusanci a Afirka

Schwikowski Martina MNA
August 25, 2020

Wani bincike da aka gudanar ya nuna yawan mutane da ke sha'awar koyon harshen Jamusanci a Afirka musamman a kasashen Kenya da Cote d'Ivoire na karuwa, wannan shi ne abin da shirin Taba Ka Lashe ya duba.

https://p.dw.com/p/3hTsd
Unterricht im Fach Deutsch als Zweitsprache
Hoto: picture-alliance/dpa

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake gudanar da wata gasa ta duniya kan nazarin harshe wanda cibiyar raya al'adun Jamus ta Goethe Institut ta shirya. Cibiyar raya al'adun Jamus ta Goethe da sashen kula da ilimin makaratu na ketare da cibiyar raya Ilmi da musayar dalibai ta Jamus DAAD da kuma tashar Deutsche Welle suna daga cikin wadanda suka gudanar da aikin tattara alkaluman. Kuma sakamakon ya nuna harshen Jamusanci na kara samun farin jini a matsayin bakon harshe a kasashen ketare. Shekaru biyar da suka wuce yawan masu koyon Jamusanci a Afirka ya karu daga kashi bakwai zuwa kashi goma cikin dari. Ko da yake a wasu kasashen sauyin alkaluman da aka samu ba shi da yawa. To amma a Cote d'Ivoire da ke yammacin Afirka da kuma Kenya a gabashin Afirka an sami gagarumin kari na masu koyon Jamusanci. Wannan dai wani haske da ke kara karfafa kima da martabar Jamus a idanun duniya. Hasali ma alkaluman bincike da aka gudanar kan harshen Jamusanci a kasashen ketare na duniya a wannan shekarar ta 2020 wanda ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta kaddamar, sun nuna mutane fiye da miliyan 15 da dubu 400 a sassa dabam-dabam na duniya suke koyon harshen Jamusanci kuma daga cikin wannan adadi mutane miliyan daya da dubu dari shida suna zaune ne a Afirka.

Fahimtar al'adun Jamus da Jamusawa sai ka karanci harshen Jamusanci

Deutschland Rheinstetten | Deutschunterricht
Hoto: Imago Images/G. Alabiso

Wani dalili da ya sa Jamusancin ke kara samun tagomashi shi ne yadda a fannonin kasuwanci da dama a Afirka kamar na yawon bude ido da kamfanonin ketare da ke hulda da Jamus, ake samun karuwar bukatar wadanda suka iya Jamusanci. A yanzu dai manufar koyon Jamusanci ta sauya daga yin karatu kawai a Jamus. Idan kana so ka yi karatu ka kuma yi aiki a Jamus, to kuwa kana bukatar lakantar harshen. Ba wai ya zama wajibi ba ne amma karin tagomashi ne. Kuma dama ce ta fahimtar Jamus da al'adun Jamusawa.