Kotun Venezuela ta umurci a kamo dan takarar adawa
September 3, 2024Lauyan gwamnatin kasar wanda ya bukaci kotu ta amince da wannan bukata ya zargi Mr. Gonzalez da aikata laifuka masu nasaba da ta'addanci da cuwa-cuwa da gurza takardun boge domin cimma wata manufa, inda kotun ta amince da bukatar hakan saboda girman laifukan da ake zargin dan siyasar da aikatawa.
Matakin dai ya biyo bayan takaddamar da ta dabaibaye sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Yulin da ya gabata a Venezuela, inda hukumar zabe ta ayyana shugaba mai ci Nicolas Maduro a matsayin wanda ya lashe zabe duk da ikirarin da jam'iyyun adawa suka yi cewa suna da takardun da ke nuna cewa Mr. Gonzales ne ya samu kuri'u masu rinjaye.
Tun bayan sanar da sakamakon zaben, 'yan kasar sun nuna rashin amincewarsu ta hanyar zanga-zanga, yayin da kasar Amurka da wasu kasashen Latin Amurka gami da kungiyar tarayyar Turai suka suka ce an tabka magudi a zaben kuma a wurinsu dan takarar adawa Gonzalez ne ya lashe zaben.