1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Turkiyya ta yanke hukuncin dauri ga 'yan jarida

Gazali Abdou Tasawa
April 26, 2018

Wata kotun Turkiyya ta yanke hukuncin zaman gidan wakafi ga 'yan jaridar mujalla adawa ta Cumhuriyet bayan shafe lokacin ana sauraron kara.

https://p.dw.com/p/2wgxB
Türkei - Haftstrafen für Cumhuriyet-Journalisten in Istanbul
Hoto: picture-alliance/AP/C. Ozdemir

Wata kotun kasar Turkiyya ta yanke hukuncin zaman gidan wakafi na shekaru biyu da rabi zuwa sama da shekaru takwas ga wasu 'yan jarida 14 na mujalla adawa ta Cumhuriyet. Bayan share watanni tara tana gudanar da zaman shari'ar wanda ake kallo a matsayin wani zaman shari'a tantance matsayin 'yancin aikin jarida a kasar ta Turkiyya, kotun birnin Silivri na kusa da birnin Istanbul ta yanke wa 'yan jaridar wannan hukunci ne bayan da ta same su da laifin taimaka wa wasu kungiyoyin ta'adda.

Daga cikin 'yan jarida da kotun ta yanke wa wannan hukunci sun hada da Akin Atlay shugaban jaridar ta Cumhuriyet da editan jaridar Murat Sabuncu da kuma wasu shahararrun 'yan jaridar kasar ta Turkiya kamar Ahmet Sik da Kadri Gürsel ko kuma dan jaridar nan mai yin zanan barkwanci Musa Kart.

Sai dai jaridar ta Cumhuriyet ta bayyana hukuncin kotun a matsayin abin kunya kana mataki ne da zai yi munmunan tasiri ga 'yancin aikin jarida a kasar.