1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Kotun EU ta gano yadda Rasha ta yi kisan gilla

September 21, 2021

Kotun Kare Hakkin Dan Adam ta Tarayyar Turai ta ce ta gano cewa an yi amfani da wasu jami'an kasar Rasha wurin yi wa tsohon mai adawa da gwamnatin kasar Alexander Litvinenko kisan gilla a Birtaniya. 

https://p.dw.com/p/40c3s
Grab von ex-KGB Agent Alexander Litvinenko in London
Hoto: Toby Melville/REUTERS

Alexander Litvinenko ya rasu a shekara ta 2006 bayan kurbar wani shayi da aka barbada wa guba a Millennium Otel da ke Birtaniya. Kafin kisan gillar da aka yi ma sa, Litvinenko ya yi wa gwamnatin Rasha aikin samar da tsaro a hukumar tsaron kasar. Daga baya ne kuma tsohon jami'an ya koma Birtaniya ya rinka caccakar gwamnatin Rasha.


Sai dai hukumomin Rasha sun jima suna nesanta kan su da kisan gillar da aka yi wa Alexander Litvinenko wanda ya yi kaurin suna wurin kushe  hukumar leken asirin Rashan.