Kotun shariár laifukan yaki za ta bada sammaci | Labarai | DW | 29.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun shariár laifukan yaki za ta bada sammaci

Kotun kasa da kasa dake Hague wadda ke shariár laifukan yaki ta sanar da cewa nan ba da jimawa ba, zata bada takardar sammaci don kamo wasu mutane da ake zargi da laifukan yaki a kasar Congo. Babban mai gabatar da kara Luis Moreno Ocampo yace tuni masu bincike suka dukufa domin tantance bayanai a game da kisan kare dangi da ake zargin wasu kungiyoyin yan tawaye a jamhuriyar dimokradiyar Congo. Kotun kasa da kasar wadda aka kafa ta a shekara ta 2002 domin shariár manyan laifukan yaki, ta gabatar da sammacin ta na farko ta danko shugabanin kungiyar LRA ta kasar Uganda wadanda aka zarga da haddasa taása a arewacin kasar. Bugu da kari kotun ta kuma kaddamar da binciken laifukan yaki a lardin Dafur na kasar Sudan.