Kotun Nijar ta saki ′yan fafutuka | Labarai | DW | 29.09.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun Nijar ta saki 'yan fafutuka

Wata kotu a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar ta sallami 'yan fararen hular nan da gwamnatin kasar ke tsare da su kusan watanni shida. 

Rahotanni sun ce a wannan Talata kotun ta saki Maikoul Zodi shugaban kungiyar fararar hula ta "Tournon la page" da Halidou Mounkaila da Moudi Moussa biyo bayan tuhumarsu da yunkurin tada zaune tsaye ta hanyar shirya zanga-zanagar da hukumomi suka haramta.

Ali Idriss daya daga cikin fitattun 'yan fafutuka na Jamhuriyar ta Nijar ya shaida wa wakilinmu na Yamai Mamman Kanta cewa kotu ta saki 'yan farar hular bisa hujjojin da lauyoyi suka gabatar mata.