Kotun Najeriya ta wanke Saraki | Labarai | DW | 14.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun Najeriya ta wanke Saraki

Kotun da'ar ma'aikata ta wanke shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki, kan zargin boye gaskiyar kadarorin da ya mallaka.

An dai fara shari'a da Saraki watanni shida da darewarsa kujerar shugabancin majalisar, kafin daga bisani aka kwashe sama da shekara guda ana shari'ar a Kotun da'ar ma'aikatar kasar.

Alkalin kotun mai shari'a Danladi Umar, ya bayyana cewa lauyoyin gwamnatin Najeriya da ke tuhumar wanda aka zarga a shari'ar, sun gaza gamsar da kwararan hujjoji da zai tabbatar da zargin laifin da ake wa Saraki.

A ranar 4 ga wannan watan Yunin ne, shugaban majalisar dattawan Najeriyar ya shigar da karar da ke bukatar wanke shi daga laifin da ake tuhumarsa akai.