Kotun koli a Amirka ta amince da auren jinsi | Labarai | DW | 26.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun koli a Amirka ta amince da auren jinsi

Alkalai biyar ne daga cikin tara na kotun kolin suka amince da ba wa 'yan Luwadin da 'yan Madigo damar su auri juna a Amirka karkashin doka.

Shugaba Barack Obama na Amirka ya bayyana gamsuwa da hukuncin kotun koli a kasar wacce ta ba wa 'yan Luwadi da Madigo damar za su iya yin aure a hukumance karkashin dokar kasar ta Amirka.

Shugaban ya bayyana hukuncin kotun a matsayin wani abu da zai samar da sauyi a zamantakewar al'ummar kasar, wani abu da ba a tsammata ba a nan kusa.

A cewar shugaban wannan wata nasara ce da masu wannan bukata suka dade suna muradin gani, bayan kwashe gwamman shekaru suna fafutika.

Ya ce "A wannan safiya kotun koli bayan nazari karkashin kundin tsarin mulkin kasa ta amince da auren jinsi babu banbanci ga abinda ya shafi aure a kasar, wannan ya nuna cewa duk al'ummar kasar Amirka na da dama ce iri daya suna samun kariya karkashin doka".

Alkalai biyar ne daga cikin tara na kotun kolin suka amince da ba wa 'yan luwadin da 'yan madigo damar su auri juna.

Wannan hukunci kuma na nufin cewa jihohi 14 da suka haramta wannan aure za su janye hukuncinsu, bayan da kotun kolin ta amince da wannan aure a baki dayan kasar.