Kotun kasa da kasa ta bayar da umarnin cafke mutane biyu a Sudan | Labarai | DW | 02.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun kasa da kasa ta bayar da umarnin cafke mutane biyu a Sudan

Kotun dake sauraran miyagun laifuffuka ta kasa da kasa dake birnin Hugue, ta bayar da umarnin cafko daya daga cikin ministocin kasar Sudan da kuma shugaban kungiyyar yan tawayen nan ta Janjaweed.

Kotun tace ta zartar da wannan hukuncin ne don zargi da take musu da hannu a laifukan yaki da yaki ci yaki cinyewa, a yankin Darfur na kasar ta Sudan.

Kasar dai ta Sudan ta nuna alamun kin aiwatar da wannan bukata ta kotun kasa da kasar, ta hanyar kin cafke mutane biyun da ake nema ruwa a jallon.

Kafafen yada labarai dai sun rawaito mai gabatar da kara na kotun kasa da kasar, Mr Luis Moreno na cewa, abune daya zama wajibi akan mahukuntan na Sudan su kaamo mutanen biyu da ake tuhuma da wanann laifi.

Ana dai zargin Harun da kuma Ali Kushyab ne da caji 51, dake da nasaba da miyagun ayyuka na yaki kann bil adama, a yankin Darfur dake wannan kasa.