Kotun ICC za ta binciki magoya bayan shugaban Cote D′ivoire | Labarai | DW | 04.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun ICC za ta binciki magoya bayan shugaban Cote D'ivoire

Ƙungiyar Human Rights Watch ta ce za a binciki na kusa da shugaba Alassane Ouattara waɗanda suke da hannu a tashin hankali da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa tsakanin shekarar 2010 zuwa 2011.

Alassane Ouattara, Präsident Elfenbeinküste

Shugaba Alassane Ouattara

Kotun da ke hukunta masu aikata manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa ICC za ta kara zurafafa bincikenta kan rikicin da ya biyo bayan zaɓen shugaban kasa da ya rufta ƙasar Ivory Coast cikin rudani tsakanin shekarar 2010 zuwa 2011, ciki aikin kuwa za a binciki 'yan gani kashe ni ga shugaba Alassane Ouattara da ake zarginsu da aikata laifuka na take hakkin bil'Adama kamar yadda Ƙungiyar Human Rights Watch ta bayyana a ranar Talatan nan.

Tun dai a shekarar 2011ne mai gabatar da ƙara a wannan kotun da ke da sansani a birnin Hague Fatou Bensouda, take bibiyar rikicin da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa a Ivory Coast bayan da tsohon shugaba Laurent Gbagbo yaki amincewa da shan kayi a zaɓen da suka fafata da shugaba Alassane Ouattara.